News
Gobara Ta Tashi A Jami’ar Northwest Dake kofar Nasarawa A Kano

Rahotanni na nuni da cewa wata gobara ta tashi a jami’ar Northwest da ke Kofar Nasarawa, birnin Kano.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wutar ta fara ci ne a safiyar yau, inda ta fara bazuwa cikin gaggawa, Yanzu haka hayaƙi ya turnike ginin jami’ar da aka fi sani da gidan Ado Bayero.
Jami’an tsaro da na kashe gobara sun isa wurin domin dakile yaduwar gobarar, sai dai har yanzu ba a tabbatar da musabbabin tashin wutar ko asarar da aka tafka ba.