News
Gidauniyar Barau Cares Ta Samar da Kayan Sallah Ga Yara Marayu a Tarauni, Kano
A wani bangare na kokarinta na tallafa wa marayu da mabukata, Gidauniyar Barau Cares ta raba kayan Sallah ga yara marayu a unguwar Tarauni da ke jihar Kano.
Da yake jawabi a yayin taron rabon kayan, Daraktan Shirye-Shiryen Gidauniyar, Kwamarad Muhammad Sani Garba, ya bayyana cewa manufarsu ita ce su ji yadda yaran za su bayyana murnarsu da farin cikinsu game da wannan tallafi. Ya kara da cewa a baya ma, a lokacin azumin watan Ramadana, gidauniyar ta raba kayan abinci da kudade ga mazauna unguwar Hotoron Dan Marke Kankare.
Dan Bijilanti Ya Harbe Kansa Yayin Da Yake Kokarin Cafke Wani A Abuja
Kwamarad Muhammad Sani Garba ya tabbatar da cewa gidauniyar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi domin yin koyi da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa, Sanata Barau Jibril Maliya.
Haka nan wasu daga cikin manyan bakin da suka halarta, Hajiya Yahanasu Ummah Gidan Kara da Alhaji Auwalu Maba, sun taya yaran murna bisa wannan tagomashi da suka samu daga gidauniyar.
Wasu daga cikin yaran da suka amfana da tallafin, kamar Amina Muktar da Usaini Muhammad, sun bayyana jin dadinsu da kuma godiya bisa wannan taimako da suka samu.
An kammala taron cikin farin ciki da annashuwa, inda aka gudanar da liyafar tande-tande da lashe-lashe ga yaran tare da daukar hoto na bai daya domin tunawa da wannan rana maimuhimmanci.
