Connect with us

News

‎Ana Zaman Ɗar-ɗar A Ƙofar Na’isa Bayan Dawowar Faɗan Daba

Published

on

Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano

 

An sake samun rikicin daba mai tsanani a unguwannin Kofar Na’isa da Kofar Dan-Agundi a birnin Kano, lamarin da ke kara tayar da hankalin jama’a tare da haddasa asarar dukiya da lalacewar zaman lafiya a yankin.

Advertisement

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa rikicin ya sake ɓarkewa ne da daren Alhamis, yayin da matasa suka mamaye tituna suna tada hankula. Shedun gani da ido sun ce fiye da motoci da babura goma ne aka lalata, tare da jefa jama’ar da ba su da hannu cikin halin tsoro da fargaba.

Ƙananan Hukumomi 293 A Jihohi 30 Za Su Fuskanci Ambaliya Mai Tsanani A 2025 —Gwamnatin Tarayya 

Wani mazaunin Kofar Na’isa, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya bayyana damuwarsa kan yadda rikicin ke ci gaba da gudana ba tare da tsayawa ba. “Laifin iyaye ne da kuma wasu daga cikin manyan unguwa, saboda ana zargin suna marawa wadannan matasa baya, har ma suna hana hukuma ɗaukar mataki,” in ji shi.

Advertisement

Fadan, wanda ya fara tun kafin ƙaramin Sallah, ya rikide zuwa rikici mai zafi da har yanzu ba a samu maslaha ba. Mazauna yankin na bayyana damuwa kan yadda dukiyoyin da ba su da alaƙa da rigimar ke shiga cikin barnar, ciki har da gidaje da shaguna.

Hukumomin tsaro na ci gaba da sintiri a yankin tare da ƙoƙarin shawo kan lamarin, sai dai har yanzu ba a bayyana wani cikakken shiri ba na kawo karshen wannan fitina da ke ci gaba da barazana ga zaman lafiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending