Connect with us

Entertainment

Rigima Tsakanin Mawaƙa: An Kama Portable Bayan Ƙorafi Daga Osupa

Published

on

Guardian Youth Portable 23 3 24
Spread the love

Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kwara ta kama fitaccen mawaƙin zamani Habeeb Okikiola Badmus, wanda aka fi sani da Portable, sakamakon rikicinsa da shahararren mawaƙin Fuji, Okunola Saheed, wanda aka fi sani da Saheed Osupa.

An kama Portable ne da yammacin Lahadi a garin Abeokuta, Jihar Ogun, bisa umarnin sammacin kotu da ke zamanta a Ilorin, bayan samun ƙorafi daga Osupa dangane da zarge-zargen cin mutunci, barazanar kisa, tayar da fitina, da kuma amfani da munanan kalamai a bainar jama’a.

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum Biyu, Sun Yi Garkuwa Da Mutum 50 A Ƙauran Namoda

Kakakin rundunar ƴan sanda na Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa an samu shaidun da suka tabbatar da buƙatar kama mawaƙin, wanda hakan ya sa jami’ai suka je Abeokuta domin kamo shi.

Advertisement

> “Tuni da isarsa Ilorin, aka fara gudanar da bincike tare da tambayoyi a gaban lauyoyin ɓangarorin biyu,” in ji SP Ejire-Adeyemi.

Rahotanni sun nuna cewa rigimar ta samo asali ne daga sabanin ra’ayi kan mallakar waƙa, inda Portable a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, ya furta kalaman da suka jawo cece-kuce. A cikin bidiyon, Portable ya bayyana cewa, “Kuɗi ne ya jawo faɗan!” yana mai korafi kan wata alƙalumma da yake ganin an tauye masa.

Bayan fushin jama’a da suka yi tir da kalamansa, Portable ya sake wani bidiyo yana neman afuwa daga Osupa, yana cewa:

Advertisement

> “Sarki Saheed Osupa, babana, don Allah ka gafarta min. Ka ɗauke ni kamar ɗanka ka horar da ni.”

Sai dai, Osupa ya yi watsi da neman afuwar, yana mai cewa dole a bi doka wajen hukunta abin da ya faru.

Rigimar, wadda ta fara ne a kafafen sada zumunta, yanzu ta koma zuwa zauren kotu, inda ake sa ran gurfanar da Portable a gaban shari’a nan ba da jimawa ba.

Advertisement

Yanzu dai idanu na kallon yadda wannan rikici zai ƙare – ko dai a samu sassauci, ko kuma a ɗauki matakin doka bisa ƙa’ida.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *