Connect with us

News

An Kama Mahaifi Da Laifin Jiwa Ɗansa Rauni Saboda Zargin Satar Biskit A Kaduna

Published

on

biskit
Spread the love

Hukumar kula da jin daɗin al’umma da walwala ta Jihar Kaduna ta ceto wani yaro ƙarami, Abubakar Sani, mai shekaru bakwai da haihuwa, wanda ya gamu da mummunan rauni a hannun mahaifinsa, Sani Tanimi Maishago, bisa zargin satar biskit a karamar hukumar Lere.

Rahotanni sun nuna cewa Maishago, tare da taimakon matar sa ta biyu, ya ɗaure ƙafafun Abubakar kafin ya zuba musu ruwan zafi, sannan suka kulle shi a ɗaki na tsawon fiye da kwanaki ashirin ba tare da isasshen abinci ko kulawa daga likita ba. Wannan danyen aiki ya jawo munanan raunuka a ƙafafun yaron, lamarin da ya haddasa yaduwar cututtuka masu ƙwari saboda zargin satar biskit.

Yadda Ganduje Ya Maida Hankali Wajen Gina Jam’iyyar APC Don Tunkarar Zaben 2027

Jami’an hukumar jin daɗin al’umma sun kai ɗauki, inda aka garzaya da Abubakar zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko. A nan ne likitoci suka tabbatar da bukatar cire masa ƙafafunsa duka domin ceto rayuwarsa.

Advertisement

Kwamishinar Ma’aikatar Jin Daɗin Al’umma da Ci Gaban Zamantakewa, Hajiya Rabi Salisu, ta ziyarci yaron a asibitin, inda ta bayyana cewa gwamnati ba za ta yi wata-wata ba wajen ganin an hukunta masu laifin.

“Za mu tabbatar da cewa an yi adalci ga Abubakar, domin hakan ya zama darasi ga duk wani uba ko uwa da ke tunanin azabtarwa ita ce hanyar gyaran yaro,” in ji Hajiya Salisu.

Shugaban asibitin, Dr. Abdulkadir Musa, ya bayyana cewa Abubakar na bukatar kafa na roba domin ci gaba da motsi, yana mai gargadi ga iyaye da su daina aikata muggan laifuka ga ‘ya’yansu.

Advertisement

DAILY REALITY ta ruwaito cewa wannan lamari ya sake ƙarfafa kudirin gwamnatin jihar Kaduna wajen yakar duk wani nau’in cin zarafin yara, tare da tabbatar da cewa doka ta yi aiki ba tare da rangwame ba ga masu aikata irin waɗannan laifuka.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *