News
Isa Abdullahi Gwamya Ya Kaddamar da NIU Don Gina Matasa da Inganta Najeriya
A wani gagarumin mataki na ci gaba, Isa Abdullahi Gwamya, wanda ya kafa ƙungiyar Nigerian Investment Unique (NIU), ya kaddamar da shirin da ke da burin gina rayuwar matasa da kuma bunkasa ci gaban Najeriya baki ɗaya.
A wajen kaddamarwar, Isa Abdullahi Gwamya ya bayyana NIU a matsayin wata ƙungiya da za ta kasance dandali na haɗin gwiwa domin tallafawa matasa da masu burin samun ci gaba, ba tare da la’akari da matsayin ilimi ko asalinsu ba. Ya ce manufar ƙungiyar ita ce haɗa matasa da damammaki a fannoni daban-daban, tare da haɗa su da ƙwararru daga sassa kamar ‘yan kasuwa, masana, likitoci, lauyoyi, jarumai, sojoji, ‘yan jarida da ‘yan siyasa.
Babu Shirin Hana Shigo Da Na’urorin Sola Zuwa Najeriya — Gwamnatin Tarayya
Isa ya jaddada cewa NIU za ta kasance cibiya ta zamani wadda za a iya samunta ta kafafen sada zumunta da yanar gizo, domin sauƙaƙa hulɗa da musayar bayanai. Ya ce wannan dandali zai taka muhimmiyar rawa wajen rage matsalar rashin aikin yi, dakile aikata laifuka da kuma inganta rayuwar al’umma.
Ya bayyana cewa babban sharadi na shiga NIU shi ne kasancewa da burin rayuwa mai kyau, nuna ƙwazo, da kishin ƙasa. Isa ya kuma bukaci goyon bayan gwamnatin tarayya da na masu zaman kansu domin tabbatar da cikar wannan burin.
A cewar Isa, NIU za ta zama ginshiƙi wajen bai wa matasa damar amfani da basirarsu da ƙwarewarsu don ƙirƙirar sabbin damammaki, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ci gaba mai ɗorewa ga Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
“In muka haɗa kai domin ganin wannan mafarki ya zama gaskiya, Najeriya za ta zama abin koyi ga duniya,” in ji Isa Abdullahi Gwamya.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
