Connect with us

News

Babu Shirin Hana Shigo Da Na’urorin Sola Zuwa Najeriya — Gwamnatin Tarayya

Published

on

SOLAR PANEL 1536x1152

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a halin yanzu babu wani shiri na dakatar da shigo da na’urorin samar da hasken rana (solar panels) zuwa Najeriya.

Shugaban Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA), Injiniya Abba Aliyu, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar PUNCH . A cewarsa, duk da cewa an fara kera na’urorin solar a cikin gida, adadin da ake samarwa bai kai matakin da zai iya biyan bukatar kasa gaba ɗaya ba.

Advertisement

Ƴan Bindiga Sun Sace Matar Dagaci Da Diyarsa A Kaduna

“Ko da yake mun fara kera na’urorin solar a Najeriya, amma har yanzu ba mu da isassun adadi da zai wadatar da bukatun ‘yan kasa. Saboda haka, gwamnati ba ta shirin hana shigo da solar a yanzu,” in ji shi.

A kwanakin baya, Ministan Kimiyya, Fasaha da Bincike, Uche Nnaji, ya bayyana cewa gwamnati na aiki tukuru don karfafa masana’antun cikin gida, ta yadda za a rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Advertisement

Ministan ya bayyana cewa Najeriya na da cibiyoyin masana’antu kamar NASENI da kuma wasu ‘yan kasuwa masu zaman kansu da ke kera kayayyakin solar. Ya ce aiwatar da Dokar Shugaban Ƙasa mai lamba 5 zai taimaka wajen karfafa wadannan masana’antu da rage shigo da kayayyakin waje.

Sai dai Injiniya Aliyu ya jaddada cewa har sai an tabbatar da wadatuwar masana’antu a cikin gida kafin a ɗauki matakin dakatar da shigo da solar.

Advertisement

“Ba za mu hana shigo da na’urorin solar ba a yanzu. Muna kokarin karfafa masana’antun cikin gida, amma ba mu da isasshen ƙarfin samarwa a halin yanzu,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa sama da naira biliyan 200 ake kashewa a kowace shekara wajen shigo da na’urorin solar zuwa kasar, inda ya ce ana kokarin gina masana’antun kera batirin lithium a Najeriya, musamman a birnin Legas da wasu sassa na ƙasar.

Advertisement

Ya bayyana cewa haɗin gwiwa da kamfanonin kasa da kasa na kan tafiya da nufin bunkasa masana’antar samar da kayayyakin hasken rana a gida, domin karfafa tattalin arzikin kasa da rage dogaro da kayayyakin waje.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending