Connect with us

News

Jami’an Hukumar EFCC Sun Kama Ma’aikacin Jirgi Da Abokinsa  Kan Makudan Kuɗaɗen Waje A Kano 

Published

on

1745863446335

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta kama mutum biyu a filin jirgin sama na Kano, bayan da aka gano dubban dalolin Amurka da sauran kuɗaɗen ƙasashen waje da aka ɓoye cikin jaka.

A cewar wata sanarwa da EFCC ta fitar a ranar Litinin, jami’an hukumar kwastam sun gano dala $86,500,305 da kuma Riyal 305,150 da aka ɓoye cikin zannuwan gado a cikin jaka, yayin da wani ma’aikacin filin jirgin sama mai suna Sale Bala ya yi ƙoƙarin ɗaukar ta a ranar Lahadi.

Advertisement

‎Kotun Soji A Nijeriya Ta Yanke Wa Wani Soja Hukuncin Kisa 

Sanarwar ta ce bayan gudanar da bincike, an kama Sale Bala tare da wani Abdullahi Tahir, wanda ake zargin shi ne zai karɓi jakar bayan an gama tantance ta.

EFCC ta bayyana cewa kuɗaɗen da kuma waɗanda ake zargin suna tsare a hannunta, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Advertisement

Wannan kama na ɗaya daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin dakile safarar kuɗaɗe da sauran laifukan da suka shafi tattalin arziƙi a ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending