News
CREDICORP Ta Kaddamar Da Shirin Wayar Da Kai Kan Lamuni Mara Ruwa A Kano

Hukumar bayar da lamuni ga masu amfani da kayayyaki ta ƙasa, wato CREDICORP, ta kaddamar da wani sabon shirin wayar da kai kan hanyoyin samun lamuni mara ruwa domin sauƙaƙa rayuwa ga ƴan kasuwa da ɗaiɗaikun mutane a jihar Kano.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a birnin Kano, inda Babban Daraktan hukumar, Uzoma Nwagba, ya bayyana cewa wannan shiri na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
An Sanya Ladan Naira Miliyan 5 Ga Wanda Ya Bankado Fursunonin Da Suka Tsere
> “Muna ƙoƙarin kawo ƙarshen tsarin ‘cash-and-carry’ da ya jima yana hana jama’a damar mallakar kayayyakin bukata. Maimakon a jira a tara kuɗi tsawon lokaci, mutum zai iya samun kayansa cikin gaggawa ta hanyar amfani da lamuni mara ruwa,” in ji Nwagba.
Ya ƙara da cewa, har yanzu akwai wasu da ke kallon neman lamuni a matsayin wata alama ta talauci ko matsala, amma ya jaddada cewa idan aka sarrafa lamuni yadda ya kamata, zai inganta rayuwar jama’a matuƙa.
Sai dai ya bayyana cewa CREDICORP ba ta bayar da lamuni kai tsaye ba, sai dai ta hanyar haɗin gwiwa da bankuna da cibiyoyin kuɗi da gwamnati ta amince da su.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Ƴan Kasuwa ta Kwari, Alhaji Musa Umar Sanda, ya yaba da shirin, yana mai cewa lokaci ya yi da irin wannan dama za ta ƙara bunƙasa kasuwanci da rage wahalhalu.
> “Wannan dama ce ta musamman da za ta sauƙaƙa harkokin kasuwanci ga dubban ƴan kasuwa a Kano da ma wajen ta,” in ji shi.
Haka zalika, Manajan Yanki na Ecobank a Kano, Mustapha Mohammed, ya tabbatar da cikakken goyon bayan bankin ga shirin, inda ya bayyana cewa Ecobank tana da burin kai irin wannan sauƙin har ƙauyuka.
> “Haɗin gwiwar da muke da CREDICORP za ta taimaka wajen sauƙaƙa hanyoyin samun lamuni, musamman ga waɗanda ke zaune a yankunan da ba su da damar kai tsaye zuwa bankuna,” in ji shi.
Shirin wayar da kai da aka kaddamar zai kasance wani babban mataki na farfaɗo da sana’o’i da rage matsin tattalin arziki ga al’ummar jihar Kano.