News
Ƙudurin Hana EFCC Da ICPC Sarrafa Dukiyar Da Aka Kwato Ya Tsallaka Karatu Na Biyu A Majalisa
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da karatu na biyu na wani ƙudurin doka da ke neman hana hukumar EFCC da ICPC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa ikon sarrafa dukiyar da ake ƙwato daga hannun masu laifi.
Ƙudurin dokar, wanda ya samu karbuwa daga yawancin ‘yan majalisar, yana nufin a ƙirƙiri wata sabuwar hukuma da za ta riƙa kula da dukiyar da aka kwato, maimakon barin aikin a hannun hukumomin binciken.
Ƙudurin Hana EFCC Da ICPC Sarrafa Dukiyar Da Aka Kwato Ya Tsallaka Karatu Na Biyu A Majalisa
Wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka goyi bayan dokar sun ce hakan zai sauƙaƙa aikin hukumomin kamar EFCC da ICPC, domin za su maida hankali kan bincike da gurfanar da masu laifi a gaban kotu, maimakon rike dukiya.
Sai dai wasu ‘yan majalisa da suka nuna rashin amincewa da dokar sun bayyana damuwarsu cewa, cire wannan iko daga hannun EFCC da ICPC zai iya raunana ayyukansu da rage musu ƙarfi a yaƙin da suke da rashawa a ƙasar nan.
Yanzu dai ƙudurin na jiran shiga karatu na uku kafin Majalisar Dattawa ta yanke hukunci na ƙarshe, wanda zai buƙaci amincewar shugaban ƙasa kafin ya zama doka.
