Connect with us

News

INEC Za Ta Kafa Sashen AI Don Tabbatar Da Sahihancin Zaɓe

Published

on

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana shirin kafa wani sabon sashen da zai dinga aiki da Ƙirkirarriyar Basira (AI) domin inganta gudanar da zaɓe a Najeriya.

Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Talata, 22 ga Mayu, ta ce sabon sashen zai taimaka wajen sauƙaƙa harkokin zaɓe da hana yaɗuwar labaran ƙarya a kafafen sada zumunta.

Advertisement

Kamata Yayi Gwamnatin Kano Ta Kafa Hukumar Samar Da Farin Ciki, Ba Dakile Hanyoyin Farin Cikin Al’umma Ba

Kwamishinan hukumar kuma Shugaban Sashen Sadarwa da Wayar da Kan Jama’a, Sam Olumekun ne ya bayyana hakan, inda ya ce INEC ta shiga taruka daban-daban a nahiyar Afrika kan amfani da AI a harkokin zaɓe.

Ya ce ana sa ran fasahar za ta taimaka wajen rarraba kayan zaɓe, tattara bayanai, da ɗaukar matakai cikin sauri, haka kuma za ta taimaka wajen gujewa matsalolin da kan tashi a lokacin zaɓe.

Advertisement

“Hakika akwai haɗari idan aka yi amfani da Ƙirkirarriyar Basira wajen yaɗa bayanan ƙarya ko jirkita gaskiya, amma idan aka yi amfani da ita yadda ya kamata, za ta taimaka ƙwarai wajen tabbatar da gaskiya da sahihanci a tsarin dimokuraɗiyya,” in ji Olumekun.

INEC ta ce sabon sashen zai kasance ƙarƙashin Sashen Fasaha da Sadarwa na hukumar, kuma za a yi amfani da shi wajen ƙara inganta hulɗa da masu zaɓe da kuma tabbatar da sahihancin sakamakon zaɓe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending