Connect with us

News

Kamata Yayi Gwamnatin Kano Ta Kafa Hukumar Samar Da Farin Ciki, Ba Dakile Hanyoyin Farin Cikin Al’umma Ba

Published

on

IMG 20250522 WA0020

Wani mazaunin Jihar Kano, Malam Salisu Umar, ya shawarci Gwamnatin Jihar da ta kafa sabuwar hukuma da za ta mayar da hankali kan samar da hanyoyin nishaɗi da walwala ga al’umma, maimakon kawai ta takaita damar farin ciki da jama’a ke da ita.

Malam Salisu ya bayyana cewa al’ummar Kano na fama da damuwa da gajiya ta rayuwa, sabo da rashin wuraren shakatawa da ke taimakawa wajen rage irin wannan nauyi na yau da kullum.

Tsofaffin Kansilolin Zamfara Sun Koka Da Rashin Biyan Hakkokinsu

“A yau idan ka kalli fuskokin mutane, za ka fahimci cewa da dama ba su cikin walwala. Rashin guraben nishaɗi na haddasa hawan jini da damuwa,” in ji shi.

Ya ce saboda wannan gibi, matasa da dama sun koma shafukan intanet kamar TikTok domin samun nishaɗi, kasancewar babu wasu wuraren zahiri da za su je su shakata da iyalansu.

“Mutum na iya shafe awa uku yana kallon TikTok saboda yana jin daɗi, amma babu inda zai kai kansa ko iyalinsa don jin daɗi a zahiri,” a cewarsa.

Ya kuma ce yana da kyau gwamnati ta ware hanyoyin nishaɗi na halas, wadanda ba sa sabawa da doka da al’ada, domin bai wa jama’a damar jin daɗin rayuwa.

Advertisement

“Ina da tabbacin Gwamna yana da kishin al’umma. Amma ya kamata a samar da hanyoyin nishaɗi masu tsafta da suka dace, ba wai kawai a rika haramta abin da ke faranta ran mutane ba.”

Salisu ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake fifita wasu nau’o’in nishaɗi fiye da wasu, yana mai cewa:

“Ana yin koroso a gaban Gwamna, amma me ya sa ba a yin nishaɗin kauyawa a gabansa?

A martaninsa, Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Malam Abba El-Mustapha, ya ce hukumar ba ta hana nishaɗi ba, sai dai tana kokarin tsaftace fina-finai da shirye-shiryen da ba su dace da tarbiyya da al’ada ba.

“Duk abin da ake ce gyara, to akwai radadi. Shi ya sa wasu ke jin kamar an takura musu. Amma manufar mu ita ce kare tarbiyyar al’umma da tsaftace al’adu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa hukumar ta dakatar da shirye-shirye 22 daga talabijin da intanet saboda dalilan da suka shafi gyara da tsafta.

Advertisement

“Hukumar na goyon bayan nishaɗi matuƙar yana cikin tsafta tare da mutunta addini da al’ada,” in ji El-Mustapha.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending