News
Tsofaffin Kansilolin Zamfara Sun Koka Da Rashin Biyan Hakkokinsu
Kungiyar tsofaffin kansilolin jihar Zamfara da suka yi mulki tsakanin shekarar 2012 zuwa 2023 ta koka kan yadda rashin biyan hakkokinsu ya jefa mambobinta cikin mawuyacin hali.
Shugaban kungiyar reshen jihar Zamfara, Honarabul Abdullahi Gwaram, ya ce wasu daga cikin mambobin kungiyar na fuskantar matsaloli na rayuwa, inda wasu ma ke tsare a gidan yari saboda bashin da ake binsu.
Rahoto: ‘Yan Majalisa Na Cusa Ayyuka Marasa Amfani A Kasafin Kuɗi – BudgIT
A cewarsa, a wani zama da suka yi da Gwamnan jihar, ya bayyana shirinsa na biyansu dukkan hakkokinsu, lamarin da ya kara musu kwarin gwiwa cewa gwamnati na da niyyar warware musu matsalar.
Gwamnati Ta Ce Babu Alkawari
Sai dai a nata bangaren, gwamnatin jihar ta ce babu wani alkawari da aka yi tsakaninta da kungiyar.
Babban mataimaki na musamman ga gwamna a kan kafafen yada labarai da al’amuran yau da kullum, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce gwamnati ba ta yi wata yarjejeniya da tsofaffin kansilolin ba.
Duk da haka, kungiyar tsofaffin kansilolin ta bayyana cewa a shirye take ta koma teburin tattaunawa da gwamnatin jihar domin neman mafita ga matsalarsu.
