Politics
Shirin Ƴan Adawa Na Kawar Da Tinubu A 2027 Ya Fara Tangal-tangal

Shirin da manyan ‘yan adawa ke yi na haɗa kai domin su kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 na fuskantar cikas, bayan da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya ce zai tsaya takara da kansa.
Obi, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a WhatsApp, inda yake tattaunawa da wasu matasa magoya bayansa.
Kwankwaso Da Ganduje Su Ne Matsalar Da Ke Hana Jihar Kano Ci Gaba – Cewar Sheikh Ibrahim Khalil
A cewarsa, rikicin cikin gida da ke addabar manyan jam’iyyun adawa – PDP da LP – ya samo asali ne daga tsarin siyasar da ke aiki a Najeriya.
“Yayin mulkin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’aduwa, idan an samu matsala a jam’iyya, sai ya kira shugaban INEC ya ce masa ya gyara. Amma yau gwamnati na kallo ne kawai,” in ji Obi.
Ya kara da cewa idan ya samu dama zai gyara tsarin da ke haifar da irin wadannan matsaloli.
Da aka tambaye shi ko a wace jam’iyya zai tsaya a 2027, Obi ya ce: “Ni dan jam’iyyar Labour ne, kuma zan ci gaba da tsayawa takara a cikinta.”
Peter Obi ya kuma yi kira ga jama’a da su kare kuri’unsu a zabe mai zuwa. Ya ce ko da wakilan jam’iyya sun karɓi cin hanci, hakan ba zai yi tasiri ba idan jama’a suka kare kuri’unsu.
Tsohon gwamnan jihar Anambra din ya bayyana cewa akwai bukatar a samar da lokaci na ritaya ga ‘yan siyasar da ke neman mulki a kai a kai.
Maganganun Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa manyan ‘yan adawa kamar Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai na kokarin kafa kawance domin su kara da Tinubu a 2027.
Sai dai ficewar Obi daga wannan shiri na iya raunana haɗin gwiwar.