News
Rikici Kan Tambarin Shayi Na Barazana Ga Aikin Sama Da Matasa 500 A Kano
Wani rikicin kasuwanci da ya kunno kai a jihar Kano, ya fara haifar da barazana ga makomar sama da matasa 500 da ke samun abin dogaro a wani kamfani mai sarrafa shayi, sakamakon gardama kan mallakar tambarin shayi da ake amfani da shi.
Matasan yan kasuwar Yusuf Imam Yahaya, da kuma Zaharaddeen Imam Yahya, Wanda su ne Shugabannin kamfanin Y&Z Black Tea, ya bayyana yadda suke fuskantar matsin lamba daga wani babban kamfani da ke zargin su da kwaikwayon tambari, duk da cewa sun bi doka kaf.
Yadda Rikici Kan Tambarin Shayi Ke Barazana Ga Rayuwar Ma’aikata 500 A Kano
“Mun yi rijista da CAC, mun samu lasisi daga Hukumar Trademark, mun kuma samu sahalewar NAFDAC da SON kafin mu fara wannan sana’a,” in ji Yusuf yayin tattaunawa da manema labarai.


“Kotu Ta Ba Mu Nasara, Amma Ana Yi Biris”
A cewar Yusuf, rikicin ya kai ga gaban kotu, inda aka yanke hukunci a kan cewa Y&Z Black Tea ne ke da sahihin hurumin mallakar tambarin. Sai dai ya koka da yadda bangaren da suka shigar da kara ke ci gaba da bijirewa hukuncin kotu.
“Sun bijire wa hukuncin kotu. Maimakon haka, sai suka koma yada ƙarya a kafafen yaɗa labarai, har ma suka jawo sunan Interpol, suka kuma sa sunana da hotona a jerin masu laifi, duk saboda gardama kan tambari – ba wai laifi na aikata ba,” in ji shi.
Yusuf ya ce tambarin da ake gardama kansa ƙwararrun masu zane ne suka ƙirƙira shi, kuma akwai shaidun hakan a hukumance.

Ana Tauye Haƙƙin Matasa Masu Ƙoƙari – Yusuf
Yusuf ya bayyana cewa wannan rikici ya zarce matsalar kasuwanci, ya koma wata hanya ta tauye haƙƙin matasan Arewa da ke ƙoƙarin kafa sana’o’insu.
“Wasu daga wasu sassa na ƙasar nan sukan zo Arewa su yi kasuwanci su riba, amma idan mu matasa muka ƙirƙiri wani abu, sai a hana mu cigaba. Wannan zalunci ne,” in ji Yusuf da cike da alhini.
Ya ce kamfaninsu na bai wa fiye da ma’aikata 500 aiki kai tsaye, banda waɗanda ke cin gajiyar harkar kai tsaye daga harkar shayi da suke gudanarwa a cikin garin Kano da kewayenta.
“Idan aka ruguza kamfaninmu, rayuwar daruruwan iyalai za ta shiga mawuyacin hali. Wannan na nuni da yadda rashin aiki zai ƙara tsananta a Arewa,” in ji shi.
Duk da ƙalubalen da suke fuskanta, Yusuf da ɗan uwansa mai shekaru 29, sun ce ba za su ja da baya ba. Sun ce kafa wannan kamfani ba kawai don riba suka yi ba, sai don nuna wa duniya cewa matasan Arewa ma na da ƙwazo da hangen nesa.
“Mun kafa wannan kamfani ne don taimaka wa al’umma da ƙarfafa gwiwar matasa. Muna kira ga gwamnati, hukumomi, da kafafen yaɗa labarai da su tsaya kan gaskiya. Kada a bar masu ƙarfi su murƙushe mana mafarki,” in ji Yusuf.

