News
Jonathan Ya Samu Goyon Bayan Gwamnoni 22, Amma Ya Fadi – Ndume Ya Gargaɗi Tinubu
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce bai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a yunkurin neman wa’adi na biyu da wasu gwamnoni suka fara, yana mai cewa halin da Najeriya ke ciki bai dace da hakan ba.
Ndume ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na Channels Television a ranar Lahadi.
Bincike: DSP Barau Shine Sanata Mafi Aiki Da Tasiri A Arewa
Ya ce duk da cewa gwamnoni 22 na jam’iyyar APC sun nuna goyon baya ga Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaben 2027, shi bai goyi bayan hakan ba saboda matsin rayuwar da jama’a ke ciki.
“Ina jin tausayin Shugaba Tinubu. Gwamnoni 22 sun mara wa Jonathan baya a 2015, amma hakan bai hana shi fadi zabe ba,” in ji shi.
Ya ce a lokacin da Jonathan ke neman wa’adi na biyu, duk da irin goyon bayan da ya samu daga jam’iyyarsa ta PDP da gwamnoni, ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
“Yanzu haka ‘yan Najeriya na cikin matsanancin hali. Tattalin arziki ya tabarbare, farashin kaya ya tashi, matsalar tsaro kuma na cigaba da ta’azzara. Jama’a ba su jin dadin tsarin Renewed Hope, kuma ba su ganin haske,” a cewarsa.
Sanatan ya ce ya halarci taron da aka yi a Banquet Hall na Fadar Shugaban Kasa a ranar 22 ga Mayu, amma ya bar wurin bayan ya fahimci cewa taron goyon bayan wa’adi na biyu ne.
“Na je ne domin wani taron koli, amma daga baya sai aka koma batun kada kuri’ar murya don nuna goyon bayan wa’adi na biyu, sai kawai na fice. Amma hakan ba yana nufin na fita daga APC ba,” in ji shi.
Ya ce duk da kasancewarsa a jam’iyyar APC, ba dole ba ne ya yarda da duk wani mataki da ake dauka idan bai dace da gaskiya ko bukatun al’umma ba.
