News
Usman Alhaji Na Neman Komawa Siyasa Ta Hanyar Farfaganda — Cewar Kungiyar NDWT
Kungiyar Nigeria Democracy Working Team (NDWT) ta mayar da martani mai zafi kan kalaman da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya yi a wani taron manema labarai da ya kira tare da ƙungiyar APC Patriotic Volunteers.
A cikin jawabin nasa, Alhaji Usman Alhaji ya zargi gwamnatin Jihar Kano da rashin tsari, son zuciya da kuma gazawa wajen gudanar da mulki.
Sai dai kungiyar NDWT ta bayyana wannan zargi a matsayin “ɓatanci marar tushe da wani yunƙuri na farfaganda daga ɗan siyasa da ya rasa tasiri a idon jama’a.”
“Wannan kalamai da tsohon SSG ya yi ba komai ba ne illa yunkurin wani da ke neman komawa cikin sahun siyasa ta hanyar ɗora laifi kan gwamnati mai aiki tukuru,” in ji sanarwar kungiyar.
Kungiyar ta ƙara da cewa tun daga hawan gwamnatin Abba Kabir Yusuf, akwai tsari da manufa a aiwatar da ayyuka, musamman a fannoni kamar su ilimi, lafiya, noma da kuma ci gaban matasa.
“A zahiri, ayyuka na nan suna gudana — daga tituna, makarantu, asibitoci, har zuwa cikin gidajen jama’a. Mutane na gani da idanunsu kuma suna amfana kai tsaye.”
NDWT ta ce rashin nasarorin da Alhaji Usman Alhaji ya samu a baya a siyasa ya isa zama shaida cewa ba shi da irin kwarewar da zai soki gwamnatin yanzu.
“Tun daga lokacin da ya tsaya takarar Sanata a shekarar 2007 da 2011 — bai taba lashe zabe ba. A 2015 ma, ya fito takarar gwamna, amma daga baya ya janye sannan aka ba shi mukamin Sakataren Gwamnati (SSG).”
Kungiyar ta yi zargin cewa yanzu da ya rasa mukami da tasiri a siyasa, sai kawai ya jingina da ƙungiyoyi marasa tushe yana ta baza kalaman da ba su da tushe da ma’ana.
> “Irin wannan faɗuwa daga gwamnati zuwa kangon siyasa kan shafi lafiyar tunani. Watakila wannan ne ke sa tsohon SSG ya rika furta maganganu marasa ma’ana,” in ji kungiyar.
Daga ƙarshe, kungiyar ta bukaci jama’a da su yi watsi da kalaman Alhaji Usman Alhaji, domin kuwa gwamnatin Kano tana kan aiki kuma ci gaba na a bayyane.
“Bai kamata a yi shiru a kan irin waɗannan kalamai ba, domin yin shiru na iya nuni da amincewa. Dole ne a fuskance su da gaskiya,” in ji sanarwar.
