Connect with us

News

Kotu Ta Ɗaure Mutum Wata 6 Kan Satar Takalma A Masallaci A Kaduna

Published

on

images 6 1 612x375

Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari a Jihar Kaduna ta yanke wa wani mutum mai suna Yusuf Usman hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, sakamakon kama shi da laifin satar takalma a cikin masallaci.

An yanke masa hukuncin ne a ranar Talata, bayan da ya amsa laifin shiga masallacin ba tare da izini ba tare da satar takalman masu ibada.

Advertisement

Jami’an Tsaro Sun Kama Masu Satar Waya A Kano, Sun Kwace Babura Guda Biyu

Alƙalin kotun, Malam Kabir Muhammad, ya bai wa Usman zaɓin biyan tara ta Naira 5,000 ko kuma ya fuskanci zaman gidan yari na tsawon wata shida. Baya ga haka, kotun ta umarce shi da ya biya diyya ta Naira 150,000 ga kwamitin masallacin.

Alƙalin ya bayyana cewa idan Yusuf Usman ya kasa biyan diyyar, za a ƙara masa hukuncin shekara guda a gidan yari.

Advertisement

A yayin zaman shari’ar, jami’in ‘yan sanda mai shigar da ƙara, ASP Luka Sadau, ya bayyana wa kotu cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 13 ga watan Yuni, bayan da wasu daga cikin kwamitin masallacin suka gane masa tare da mika shi ga ofishin ‘yan sanda.

ASP Luka ya ce bayan sallar Juma’a ne Usman ya sace wasu takalma da kuɗinsu ya kai Naira 100,000, yana mai cewa ya saba zuwa masallaci a ranakun Juma’a domin satar takalma, inda daga bisani yake sayar da su a kasuwannin Monday Market da Maraban Rido.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending