News
Mazauna Dan Madanho Sun Roƙi Gwamnatin Kano Ta Gyara Masu Hanyar Su Da Ta Lalace
Mazauna kauyen Dan Madanho da ke karamar hukumar Gezawa a jihar Kano sun roƙi gwamnatin jihar da ta karamar hukuma da su gaggauta gyaran hanyar da ke haɗa kauyen da Zango, wadda suka ce ta shiga cikin matsanancin hali.
A cewarsu, lalacewar hanyar na ƙara ta’azzara musu wahalhalu, musamman idan damina ta kama, inda ake fuskantar cikas wajen shiga ko fita daga yankin.
Kotu Ta Ɗaure Mutum Wata 6 Kan Satar Takalma A Masallaci A Kaduna
A lokacin wata ganawa da jami’in yaɗa labarai na Shayar Gezawa, Jamilu Mustapha Yakasai, Ya ce al’ummar yankin sun bayyana bukatar su na ganin gwamnati ta shigo cikin lamarin domin sauƙaƙa musu sufuri da harkokin yau da kullum.
Dattijon yankin, Alhaji Isah Dan Madanho, ya ce hanyar na da muhimmanci matuƙa ga rayuwar jama’a da kuma haɓakar tattalin arziki. Ya ce:
”Hanyar nan tana haɗa ƙauyuka da dama, idan aka gyara ta, za ta taimaka wa manoma da ‘yan kasuwa sosai.”
Sai dai, duk da ƙalubalen da suke fuskanta, mazauna yankin sun bayyana godiyarsu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan wasu muhimman ayyukan da yake aiwatarwa a lafiya da ilimi da sauran fannoni.
Shugaban ƙaramar hukumar Gezawa, Alhaji Mukaddas Bala Jogana, ya shaida wa NIGERIAN TRACKER cewa yana ci gaba da bibiyar lamarin tare da ma’aikatar ayyuka ta jihar domin ganin an fara aikin gyaran hanyar.
”Ina roƙon jama’a da su kasance masu haƙuri, insha Allah aikin zai fara nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Baya ga hanyar Dan Madanho, mazauna yankin sun kuma tunatar da Gwamna Abba Kabir kan alƙawarin da ya dauka na kammala hanyar Dakata-Ranga-Bela, wadda ke da alaƙa da yankin.
Sun ce a lokacin damina, sukan fuskanci cikas sosai wajen zuwa birnin Kano saboda halin da hanyar ke ciki.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
