News
Mahaifi Yayi Ajalin Ƴar Cikinsa Mai Shekaru 18 A Kano
Al’ummar unguwar Dawakin Dakata da ke cikin birnin Kano sun shiga cikin alhini da dimuwa, bayan da wani mutumi mai suna Adamu Muhammad ya shiga hannun hukuma bisa zargin dukan ‘yarsa budurwa har ta mutu.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata, bayan da aka zargi mutumin da yi wa ‘yarsa, Zainab Adamu Muhammad, dukan kawo wuka da itace, sakamakon fushin da ya yi saboda zargin cewa tana yawan fita ta bar gida tana zaman kanta a wasu wurare.
Da yake bayani ga manema labarai, yayan marigayiyar, Yahaya Adamu Muhammad, ya ce mahaifinsu ya daure kanwarsa Zainab sannan ya ci gaba da dukanta da wani itace, duk da kokarin da mahaifiyarsu ta yi na ganin an daina. Ya ce hakan ya faru ne da dare, inda daga bisani Zainab ta rasa ranta da safiyar Talata, da misalin karfe shida na safe, ranar 17 ga Yuni, 2025.
Wani shaidar gani da ido, Muhammad Muttaka Eto, ya bayyana cewa sun shiga tashin hankali da suka isa gidan domin taimako, inda suka tarar da marigayiyar daure da sarka, tana cikin mawuyacin hali, kafin daga bisani ta ce ga garinku nan.
A cewar mahaifiyar marigayiyar, Malama Mai Jidda, ta sha rokon mijinta ya kyale yar su, amma ya ki. Ta ce daga bisani sai da ta nemi wani makwabci ya zo ya kwance Zainab, sannan ta bata ruwa domin ta sha, amma hakan bai taimaka ba, domin nan da nan lafiyarta ta tabarbare, har ta rasu.
Da lamarin ya faru ne sai jami’an tsaron unguwar Dawakin Dakata, karkashin jagorancin Kwamanda Munzali Aliyu Umar, suka shigo cikin al’amarin, inda suka tuntuɓi CSP Awaisu na ‘yan sandan yankin. Daga nan ne jami’an tsaro suka dauki matakin gaggawa na kai gawar marigayiyar zuwa asibiti tare da cafke wanda ake zargi.
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai yi nasara ba a lokacin hada wannan rahoto, domin ba a samu amsa daga wayarsa ba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
