Connect with us

News

Masarautar Gaya Ta Sauke Alhaji Usman Alhaji Daga Mukamin Wazirin Gaya

Published

on

IMG 20250618 WA0029

Masarautar Gaya da ke jihar Kano ta sauke Alhaji Usman Alhaji daga mukamin Wazirin Gaya.

Sanarwar da Masarautar ta fitar a ranar Laraba ta ce matakin ya fara aiki nan take, bisa wasu dalilai da ba za a iya kauce musu ba.

Mahaifi Yayi Ajalin Ƴar Cikinsa Mai Shekaru 18 A Kano 

Wasikar sauke shi daga mukamin, wadda aka aikewa tsohon Wazirin, na cewa an dauki matakin ne bisa wasu abubuwan da suka taso, inda Masarautar ta bukaci al’umma da su dauki lamarin da muhimmanci.

Jami’in hulda da jama’a na Masarautar Gaya, Munzali Muhammad Hausawa, ne ya sanya wa sanarwar hannu, wadda aka rabawa manema labarai a yammacin Laraba.

Alhaji Usman Alhaji ya kasance tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano a lokacin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Sakataren Masarautar Gaya, Alhaji Bello Halilu, ya ce Masarautar na godiya bisa irin gudunmawar da Alhaji Usman Alhaji ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin.

Advertisement

Sanarwar ta ce Masarautar ta yaba da goyon bayan da tsohon Wazirin ya bai wa ci gaban harkokin gargajiya da kuma raya al’adun yankin Gaya.

Masarautar ta ce matakin sauke shi wani bangare ne na ƙoƙarin tabbatar da martabar sarauta da kuma kiyaye tsarin mulkin gargajiya da aka gada tun fil azal.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending