News
Jami’an Hukumar NDLEA Sun Kama Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Naira Biliyan 2.6 A Jigawa
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) reshen jihar Jigawa ta ce ta kama miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai sama da naira biliyan 2.6 a jihar.
Kwamandan hukumar a jihar, Musa Maina, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata, inda ya ce an gudanar da samamen ne a cikin kwanaki uku da suka gabata a wasu sassan jihar Jigawa da kuma Kano.
Jami’an Hukumar NDLEA Sun Kama Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Naira Biliyan 2.6 A Jigawa
Ya ce a yayin samamen, an kama mutane uku da ake zargi da hannu a safarar ƙwayoyin, tare da kwace motoci biyu da ake zargin suna amfani da su wajen jigilar kayan.
Kwamandan ya bayyana cewa ƙwayoyin da aka kama sun haɗa da Tramadol da Pregabalin, waɗanda ya ce suna daga cikin miyagun ƙwayoyin da ke haddasa lalacewar lafiya musamman ga matasa.
Musa Maina ya ce wannan ita ce babbar nasarar da hukumar NDLEA ta samu a jihar Jigawa cikin shekarar nan, inda ya ce za su ci gaba da kai wa mabambanta wurare farmaki domin dakile safarar ƙwayoyi a yankin.
Ya ce bincike na ci gaba a kan lamarin domin bankado sauran wadanda ke da hannu a safarar, tare da ci gaba da bibiyar hanyoyin da ake amfani da su wajen shigo da ƙwayoyin cikin ƙasar.
Kwamandan ya kuma bukaci hadin kan al’umma wajen ci gaba da bayar da bayanai ga hukumar domin taimakawa wajen dakile wannan mummunar annoba ta safarar miyagun ƙwayoyi.
