News
Karamar Hukumar Rogo ta ɗauki sabon salo na ayyukan jin ƙai da ci gaba
Shugaban karamar hukumar Rogo a Jihar Kano, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo, ya bayyana cewa gwamnatin karamar hukumar za ta ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa domin amfanin al’umma da bunkasa cigaban yankin.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da ginin sabon asibiti mai gado 30 a Kadana, da ke cikin gundumar Ruwan Bago. Ya ce aikin ya samo asali ne sakamakon hadin kan jama’a da kuma daidaituwar manufofi tsakaninsu da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Farfesa Gwarzo ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sanya wa wata jami’a sunan marigayi Aminu Ɗantata
Bayan kaddamar da aikin asibitin, shugaban ya ziyarci gundumar Zarewa inda ake aikin gina azuzuwan karatu uku da ofisoshi, aikin da karamar hukumar ke daukar nauyinsa kai tsaye.
Kazalika, ya duba wasu daga cikin ayyukan wutar lantarki da aka kammala a gundumomi biyar, ciki har da Gwangwan, Falgore da Ruwan Bago. Ya bukaci jama’a da su kare kayayyakin daga lalacewa da barna.
Alhaji Abubakar Mustapha Rogo ya kuma sake jaddada bukatar da ake da ita na gina hanyar da za ta hada Doka (a Zaria, Jihar Kaduna) da Sundu, Ruwan Bago, Gwangwan har zuwa Rogo, yana mai cewa hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci da zamantakewa, musamman wajen farfado da kasuwar Sundu da sauran al’amura na rayuwa.
Ya ce: “Muna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ba mu damar aiwatar da ayyukan da suka shafi lafiya, tsaro, tattalin arziki da sauran fannonin ci gaba. Wannan dama ce da za mu ci gaba da amfani da ita domin tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar Rogo.”
Taron ya samu halartar shugaban majalisar kansiloli, kansiloli, masu kula da ma’aikatu, masu ba da shawara, shugaban jam’iyyar NNPP na karamar hukumar, magoya baya da jami’an tsaro.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
