Connect with us

News

Gine-gine Da Zubar Da Shara A Magudanun Ruwa Ke Haifar Da Ambaliya A Kano  —Masana

Published

on

FB IMG 1751931289184

Masana a fannin kula da muhalli sun bayyana cewa zubar da shara da kuma gina gidaje a magudanan ruwa na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassa na Jihar Kano, musamman a lokacin damina.

A cewar masana, wannan hali na sakaci da bin ƙa’idojin gine-gine da tsarin inganta muhalli, na hana ruwa samun sahihin hanya ta wucewa, lamarin da ke haddasa ambaliya, rushewar gine-gine, asarar kadarori da kuma yaduwar cututtuka masu nasaba da ruwa.

Advertisement

Jami’an Hukumar NAFDAC Sun Gano Lita 88,000 Na Sinadaran Haɗa Abubuwan Fashewa A Kano

Sun ce sai da hadin gwiwar gwamnati da al’umma za a iya dakile wannan matsala da ke barazana ga lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.

Masana Sun Bayyana Matakai Guda Biyar Domin Dakile Ambaliya:

Advertisement

1. Guje Wa Zubar da Shara a Magudanan Ruwa

Masana sun jaddada cewa zubar da shara a cikin magudanan ruwa na toshe hanyoyin ruwa, lamarin da ke haddasa taruwar ruwa da rugujewar gine-gine yayin ruwan sama.

Advertisement

2. Tsaftace Magudanan Ruwa Akai-akai

Sun bukaci a rika gudanar da tsaftace hanyoyin ruwa kafin lokacin damina ya zo, tare da hadin gwiwar hukumomin muhalli da al’umma domin tabbatar da ingantaccen yanayi.

Advertisement

3. Dakile Gine-gine a Hanyoyin Ruwa

Masana sun shawarci gwamnati da ta kara kaimi wajen hana gina gidaje a cikin hanyoyin ruwa da tituna, tare da rusa wadanda aka gina ba bisa ƙa’ida ba.

Advertisement

4. Shuka Itatuwa

Sun ce shuka itatuwa na taimakawa wajen shan ruwan sama da rage gudun ruwan da ke saukowa daga saman tsaunuka da rufin gine-gine.

Advertisement

5. Wayar da Kan Jama’a

Masana sun bukaci gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su ci gaba da wayar da kan jama’a ta masallatai, makarantu da gidajen rediyo dangane da illolin ambaliya da hanyoyin da za a kare kai daga barazanar ta.

Advertisement

Masana sun kara da cewa ambaliya ba wai kawai tana haddasa asarar dukiya ba ce, har ma na iya haifar da yaduwar cututtuka irin su kwalara da typhoid sakamakon gurbacewar ruwa.

Sun bukaci a sanya batun dakile ambaliya cikin ajandar gwamnati da kuma shirye-shiryen wayar da kan al’umma, domin rage aukuwar irin wadannan matsaloli a nan gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending