News
Kotu Ta Aike Da G. Fresh Gidan Gyaran Hali Na Tsawan Wata Biyar
Kotu ta aike daAbubakar Ibrahim G. Fresh gidan gyaran hali na tsawan wata biyar ko ya biya tarar Naira 200,000 bayan samunsa da laifin wulakanta Naira.
An gurfanar G. Fresh a gaban Babbar kotun Tarayya mai lamba daya dake nan Kano, bisa zarginsa da cin mutuncin kudi.
Gine-gine Da Zubar Da Shara A Magudanun Ruwa Ke Haifar Da Ambaliya A Kano —Masana
Bayan Karanta masa nan take ya amsa laifinsa.
Kotun kuma ta aike dashi gidan gyaran hali na tsawan wata biyar ko yabiya tarar Naira dubu dari biyu.
An dai same shi da watsa takardun Naira dubu dubu a shagon Rahama Sa’idu dake Tarauni yayin da suke nishadi a junansu.
FREEDOM RADIO
Advertisements
