Connect with us

News

Rikicin Kan Abinci Yayi Sanadiyyar Mutuwar Miji A Yobe

Published

on

IMG 20250724 WA0025

Rikici kan abinci ya rikide ya zama masifa a garin Abba da ke Ƙaramar Hukumar Fika a Jihar Yobe, inda wata mata mai shekaru 35 ta hallaka mijinta ta hanyar bugunsa da itace a lokacin da suka samu sabani cikin gida.

Rahotanni sun bayyana cewa matar – wacce mazauna garin Abba ce – ta dauki wani katon itacen girki ta rafka wa mijinta da shi, bayan da suka shiga muhawara mai zafi a kan yadda take amfani da abinci a gidan.

Advertisement

Kotu Ta Aike Da G. Fresh Gidan Gyaran Hali Na Tsawan Wata Biyar

Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga zargin da marigayin ya yi wa matarsa na cinye kayan abinci ba tare da kiyaye ba, wanda hakan ya fusata matar, har ta dauki matakin da ya kai ga ajalin mijin nata.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulsalam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, “Lamarin ya faru a garin Abba. Bayan samun rahoton, jami’anmu sun isa wurin tare da cafke wacce ake zargi. Mijin ya rasu nan take kafin a kai shi asibiti.”

Advertisement

SP Dungus ya ce marigayin ya bar mata biyu da ’ya’ya biyar.

A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Yobe, CP Emmanuel Ado, ya bayyana damuwarsa kan yadda rikice-rikice ke ƙaruwa a tsakanin ma’aurata, yana mai cewa akwai gagarumar buƙata na wayar da kan jama’a dangane da zaman lafiya a cikin iyali.

Advertisement

“A matsayinsu na malamai da shugabannin addini, ya kamata su dinga fadakar da jama’a kan illar tashin hankali a cikin gida, domin kaucewa abubuwan da ke janyo asarar rayuka da rugujewar zamantakewa,” in ji CP Ado.

Rundunar ’yan sanda ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, sannan wacce ake zargi za ta gurfana gaban kotu da zaran an kammala bincike.

Advertisement

SP Dungus ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar ba za ta lamunci aikata laifi ba a kowane mataki, kuma za a tabbatar da adalci ga dukkan bangarorin da abin ya shafa.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending