News
Wani Mutum Ya Mutu Yayin Da Yake Yunkurin Lalata Layin Wutar Lantarki Mai Ƙarfin 132kv
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa a Najeriya (TCN) ya ce wani mutum da ake zargi da yunkurin lalata layin wutar lantarki ya mutu a jihar Ebonyi.
Lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Yuli a kan layin wutar lantarki mai ƙarfin 132KV daga Nkalagu zuwa Abakaliki, a cewar sanarwar da kakakin TCN, Ndidi Mbah, ta fitar ranar Juma’a.
An Kama Budurwa Mai Shekara 19 Kan Zargin Ajalin Yara Biyu A Bauchi
Sanarwar ta ce an samu gawar mutumin da ya makale a saman wutar lantarki mai ƙarfin 132KV.
TCN ta ce ta sha gargadin mutane kan barazanar da ke tattare da shiga wuraren layin wutar da kuma yunkurin lalata kayayyakin wutar lantarki, inda ta ce irin wannan abu na iya rasa rai.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
