Connect with us

News

An Kama ‘Yar Najeriya A Indiya Da Kwayoyi Masu Darajar Fiye Da Naira Biliyan 6

Published

on

images 22 1

Hukumomin tsaro a kasar Indiya sun kama wata mata ‘yar Najeriya dauke da miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai kusan dala miliyan hudu, kwatankwacin sama da Naira biliyan 6.

Kamar yadda rahotanni daga kafar labarai ta Deccan Herald suka nuna, an kama matar ne a wani aiki na hadin gwiwa tsakanin Rundunar Kariya ta Jirgin Kasa (RPF), Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Kwayoyi (NCB) reshen Bengaluru, da kuma sashen leken asirin ‘yan sanda na Kurla da ke Mumbai.

Advertisement

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin binciken karbar belin wanda ake zargi da harkar kwayoyi da Kwamishina ya yi.

An kama matar, wadda ta bayyana sunanta da Doris, a cikin jirgin kasa mai lamba 12618 Hazrat Nizamuddin–Ernakulam Mangala Express, tana zaune a Coach A-2, kujerar lamba 27, tare da wani yaro da ta ce dansa ne.

Bayanai sun nuna cewa an gudanar da bincike ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda jami’an tsaro suka kai samame a dandalin jirgin kasa na Platform 7 a tashar Panvel.

Advertisement

A lokacin binciken, an gano babbar jaka dauke da fakiti biyu masu launin baki da aka lullube da filastik mai lakabi da “BINTAGE”.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan gwajin da na’urori suka yi, an gano cewa fakitin na dauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 2.002.

Advertisement

Bincike ya ci gaba inda jami’an suka gano wata karamar jakar yara mai hoton Mickey Mouse da ke dauke da fakiti biyu – daya mai rubutun “Kellogg’s Corn Flakes” da daya mai rubutun “Bongchi Perfect Roll”.

Gwajin da aka yi ya nuna cewa fakitin na dauke da methamphetamine mai nauyin kilogiram 1.488.

Advertisement

Hukumomin tsaron kasar sun ce darajar wadannan kwayoyi da aka kama ya kai Rs 36 crore, daidai da dala miliyan hudu a kasuwannin kwayoyi.

Doris ta zama mace ta biyu daga Najeriya da aka kama a kasar Indiya da laifin safarar kwayoyi cikin kasa da watanni biyu.

Advertisement

Wata majiya daga jami’an tsaron Indiya ta ce akwai karin bincike da ake gudanarwa domin gano sauran wadanda ke da hannu a wannan safarar.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending