News
Jami’an Tsaro Sama da 130 Sun Rasa Rayukansu A Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa fiye da jami’ai 100 na Community Watch Corps, da ’yan sanda 30 sun mutu a yaƙi da ’yan bindiga.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Dr. Nasir Muazu, ya bayyana haka, yana mai ƙaryata rahotannin dake yaɗuwa a kafafen sada zumunta.
Ya ce wasu na ƙoƙarin haddasa fargaba da tayar da hankali ta hanyar yaɗa bayanan ƙarya kan halin da tsaro yake ciki a jihar Katsina.
Dr. Muazu ya ce tun bayan hawan Gwamna Dikko Radda a 2023, an sami ci gaba a yaƙi da ‘yan bindiga a yankuna da dama.
Ya lissafa ƙananan hukumomi 11 da suka fi samun sauƙin hare-hare, ciki har da Jibia, Katsina, Bindawa da Kafur, yayin da ƙananan hukumomi 4 ke fama da harin.
Kwamishinan ya ce Gwamna Raɗɗa na jajircewa kan tsaro, yana karɓar rahoto daga manyan jami’an tsaro duk da raunin da ya samu.
