News
Gwamnatin Tarayya Na Biyan ‘Yan Bindiga Kudi, Na Basu Abinci — El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Malam Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin tarayya da biyan kudade tare da tura kayan abinci ga ‘yan bindiga a boye, yana mai cewa wannan dabarar “sulhu” ce ta karya wadda ke ƙara wa masu laifi ƙarfin guiwa.
A wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na tashar Channels Television, El-Rufai ya ce ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ne ke jagorantar wannan tsari.
Gwamnatin Tarayya Na Biyan ‘Yan Bindiga Kudi Tare Da Basu Abinci — El-Rufai
“Gwamnatin tarayya tana da tsari na biyan ‘yan bindiga kudade, tana kuma tura musu abinci. Wannan shirin ONSA ne, kuma muna da hujjoji a kan haka,” in ji shi.
El-Rufai ya bayyana cewa bai amince da wannan hanya ba, yana kiran ta a matsayin dabarar tsaro mai rauni da ke ƙarfafa miyagu:
“Ba zan taba biyan ‘yan bindiga kudi ko tura musu abinci da sunan zaman lafiya ba. Wannan ba dabarar tsaro ba ce, wasa ce da rayukan al’umma.
A ra’ayina, mafi kyawun ‘dan bindiga shi ne wanda aka kashe. Ya kamata mu hallaka su gaba ɗaya kafin mu yi wa wanda suka rage gyara.”
Tsohon gwamnan ya yi gargadin cewa matsalar tsaro a Arewa ba za ta gushe ba muddin gwamnati ta ci gaba da aiwatar da wannan tsarin:
“Mutanen da ke zaune a Katsina, Zamfara, Kaduna sun san gaskiya. Wannan matsalar ba za ta gushe ba muddin ana tafiya da wannan tsari,” in ji shi.
-
News21 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
