News
Kano Na Asarar Biliyan Ɗaya Duk Shekara Saboda Rashin Yin Gwanjon Tsofaffin Kayan Gwamnati
Ƙungiyar masu gwanjon kayayyaki ta Najeriya (NAA), reshen Kano, ta bayyana cewa gwamnatin jihar na asarar aƙalla Naira biliyan ɗaya duk shekara saboda rashin gudanar da gwanjon tsoffin kayayyakin gwamnati da aka cire daga ofisoshi da wuraren gyare-gyare.
Sakataren ƙungiyar a Kano, Malam Isah Deneji, ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai, inda ya zargi wasu ma’aikatan gwamnati da satar tsoffin kayayyakin da aka cire daga wurare daban-daban.
Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata
A cewarsa, duk da cewa ana cire kayayyaki kamar kujeru, na’urorin sanyaya ɗaki, da interlock daga wuraren gyare-gyare, ba a sayar da su ta hanyar gwanjo ba, sai dai ana barin wasu ma’aikata su sace su su sayar a boye.
“Mun samu rahoton cewa an sace sama da na’urorin sanyaya ɗaki guda 20 daga wurin gyaran gidan gwamnati. Idan gwamnati za ta dawo da tsarin gwanjon tsoffin kayayyaki, hakan zai rage asarar da kuma tabbatar da cewa duk kudaden da aka samu sun shiga asusun gwamnati cikin tsari,” in ji shi.
Malam Deneji ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya umarci Ma’aikatar Kuɗi da ta dawo da tsarin yin gwanjon tsoffin kayayyaki domin dakile ɓarna da satar dukiyar gwamnati. Ya kuma jaddada cewa ƙungiyarsu ƙwararriya ce da ke da lasisi da ake sabuntawa duk shekara, amma gwamnatin jihar ta daina amfani da su.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Marwan Ahmad, ya ce ma’aikatarsa ba ta da hurumin yin gwanjon kayayyakin gwamnati, inda ya nuna cewa wannan aiki ya rataya ne a kan Ma’aikatar Kuɗi.
Sai dai ya yi Allah-wadai da yadda ake kwasar kayayyakin gwamnati daga wuraren da ake gudanar da gyare-gyare. “Mun kwato interlock ɗin da darajarsa ta kai sama da Naira miliyan ɗaya, wanda aka cire daga wani wuri, daga bisani muka sake amfani da shi a wani muhimmiyar cibiyar gwamnati
,” in ji shi.
-
News21 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
