News
KAMFANONI 91: Gwamnatin Tarayya Za Ta Sayar Da Matatun Man Fetur Da Filayen Jirgin Sama Biyar Ga ‘Yan Kasuwa
Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin mika ragamar gudanar da kamfanoni da kadarori 91 ga ‘yan kasuwa ko kuma ta sayar da su, ciki har da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Steel, matatun man fetur guda huɗu da manyan filayen jiragen sama biyar.
Shugaban Hukumar Kula da Cinikayyar Kadarorin Gwamnati (BPE), Ayodeji Ariyo Gbeleyi, ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Talata. Ya ce matakin zai taimaka wajen farfaɗo da kamfanonin da suka durƙushe, jawo hankalin masu zuba jari da kuma samar wa gwamnati ƙarin kuɗaɗen shiga.
‘Yan Bindiga Sunyi Ajalin Mutum 6, Sun Sace Sama Da 130 Cikin Kwana Uku A Katsina
A cikin jerin kadarorin da abin zai shafa akwai Dandalin Tafawa Balewa (TBS), Kasuwar Bajekoli da ke Legas, matatun man fetur na ƙasa guda huɗu da kuma filayen jiragen sama guda biyar kamr yanda Jaridar BLUEPRINT ta ruwaito
Gbeleyi ya ce za a aiwatar da tsarin ne cikin gaskiya da fayyacewa bisa tanadin doka, inda za a shigo da kwararru daga fannonin kuɗi da shari’a domin tabbatar da adalci.
Ya kuma ce akwai alkhairi a tsarin, inda ya tuna da yadda mika ragamar kamfanonin sadarwa, harkokin fansho da tashoshin jiragen ruwa ga ‘yan kasuwa ya taimaka wajen dorewar ayyuka da kuma samar da fiye da dala biliyan 2.5 ga ƙasar.
-
News20 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
