News
‘Yan Bindiga Sunyi Ajalin Mutum 6, Sun Sace Sama Da 130 Cikin Kwana Uku A Katsina
‘Yan bindiga sun kashe mutane shida tare da yin garkuwa da sama da mutum 130 a hare-hare da suka kai a kauyuka daban-daban na Karamar Hukumar Sabuwa a Jihar Katsina cikin kwanaki uku.
Mazauna yankin sun ce mafi muni daga cikin hare-haren ya faru ne a kauyen Dankurmi, inda aka kashe mutane hudu ciki har da jariri, sannan aka yi garkuwa da akalla mutum 79.
Rahotanni sun ce maharan sun shafe awanni hudu suna shiga gida-gida suna kwasar mutane, inda a wasu gidaje aka sace iyaye da ‘ya’yansu baki ɗaya, a wasu kuma aka sace mata da kananan yara.
Sun kuma tafi da babura da kayan abinci. Sunayen wadanda aka kashe sun haɗa da Maharazu Sani, Awusu Shafi’u da Saminu Ibrahim.
Baya ga Dankurmi, ‘yan bindigar sun kuma kai farmaki Gamji, inda suka kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da 31, da kuma Tsaunin Jino inda aka yi garkuwa da mutum 27. An kuma kai hare-hare a Unguwar Goje, Unguwar Sani da Zagi-Zagi, inda aka yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tabbatar da adadinsu ba. Majiyoyi sun ce jimillar wadanda aka sace na iya kaiwa 200.
Wani babban jami’in gwamnati daga yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce shugabannin al’umma sun garzaya Katsina domin neman tallafi daga gwamnati. Ya ce hare-haren na baya-bayan nan na iya zama yunkurin matsa lamba daga ‘yan bindiga bayan da al’ummar yankin suka nuna shakku kan yarjejeniyar zaman lafiya da suka nemi a kulla a farkon damina.
Majiyar ta kuma bayyana cewa tun da ‘yan bindigar suka kai hari sansanin sojoji a Dankolo inda suka kashe sojoji uku, an janye dakarun daga wasu wuraren da suke tsaro, abin da ya bai wa maharan damar samun shiga cikin sauki. Al’ummar yankin na kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su dawo da dakarun domin kare kauyukan daga hare-haren da ke ta ci gaba da faruwa.
-
News20 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
