News
NAHCON Ta Ɗauki Matakan Sauye-Sauye Don Inganta Aikin Hajji
Hukumar Kula da Ayyukan Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar da ɗaukar matakan sauye-sauye domin inganta ayyuka da kuma ƙara nagartar gudanar da al’amuran hajji a Najeriya.
Sanarwar da Mataimakiyar Daraktan Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta fitar a ranar Juma’a ta bayyana cewa matakan sun biyo bayan taron hukumar karo na 14 da aka gudanar daga 26 zuwa 27 ga watan Agusta, 2025.
Tambuwal: Zan Yi Bakin Ƙoƙari Wajen Kawar Da Gwamnatin Tinubu A 2027
Daga cikin sauye-sauyen da aka amince da su har da mayar da ma’aikatan da aka aro daga wasu ma’aikatu zuwa inda aka ɗauko su tun farko. Hukumar ta raba takardun shaidar komawar su a ranar Alhamis, 4 ga Satumba, 2025. Wannan mataki, a cewar hukumar, zai taimaka wajen rage yawan ma’aikatan da ke gararamba tare da tabbatar da tsarin aiki mai inganci.
Haka zalika, hukumar ta amince da ƙarin girma ga wasu ma’aikatan da suka cancanta da kuma shirye-shiryen horaswa domin ƙara inganta kwarewar dukkan jami’an NAHCON.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya tabbatar da cewa NAHCON za ta ci gaba da gina ƙwararrun ma’aikata masu jajircewa domin tabbatar da cika nauyin da aka ɗora mata na hidimtawa alhazan Najeriya. Ya ce hukumar za ta ci gaba da kirkiro sababbin tsare-tsare da za su inganta gudanar da aikin hajji a ƙasar nan.
-
News20 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
