Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Juma’a A Matsayin Ranar Hutu 

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 19 ga Rabi’ul Awwal 1447H, wanda ya yi daidai da 12 ga Satumba, 2025, a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, ne ya fitar da sanarwar a madadin gwamnatin Kano.

Advertisement

 

Sanarwar ta ce hutun zai ba wa jama’a damar gudanar da bukin Takutaha, wanda ke nuni da cika kwanaki bakwai da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Haka kuma gwamnatin ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan dama wajen nazari da kuma koyi da kyawawan halayen Manzon Allah (SAW), tare da addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.

Advertisement

Gwamnatin ta kuma taya Musulmi murnar wannan gagarumin biki na Mauludi, tana mai fatan ya kasance alheri ga kowa da kowa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending