Connect with us

News

Jihar Kano Za ta Kaddamar da Sabon Shirin Rigakafin Rubella: Hukumar PHC Ta Wayar da Kan Iyayen Yara

Published

on

IMG 20250911 WA0006

DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN

Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kano (PHC) ta gudanar da taron wayar da kai a Asibitin Na’ibawa, domin sanar da iyaye muhimmancin Sabuwar rigakafin cutar kyanda mai bin iska, wato Rubella, wanda za a fara bayarwa daga ranar 4 zuwa 14 ga Oktoba, 2025 a fadin jihar.

Advertisement

Taron, wanda aka gudanar a dakin taron asibitin, ya samu halartar masana a fannin lafiya, malamai, shugabannin al’umma da kuma wakilan sarakunan gargajiya daga kananan hukumomi daban-daban.

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Juma’a A Matsayin Ranar Hutu 

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kano, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya ce an shirya shirin domin kare lafiyar yara daga cutar Rubella wadda ke iya haddasa nakasa da wasu matsalolin lafiya.

Advertisement

Ya ce “Muna kira ga iyaye da su tabbatar sun kai ‘ya’yansu masu shekaru tsakanin tara zuwa sha huɗu domin karɓar wannan rigakafi kyauta. Mun tanadi kayan aiki da ma’aikatan lafiya da za su gudanar da aikin a cibiyoyin lafiya da makarantun firamare a fadin jihar Kano.”

Shugabar Sashen Rigakafi ta Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Ibrahim, ta ce rigakafin Rubella na da matuƙar amfani ga lafiyar yara da mata masu juna biyu.

Advertisement

Ta ce: “Wannan rigakafi zai taimaka wajen rage barazanar cututtuka da ke shafar yara da kuma mata masu ciki, don haka muna bukatar iyaye da al’umma su ba da haɗin kai.”

Rahoton ya ce taron ya samu halartar ƙungiyoyin lafiya na duniya da suka haɗa da WHO, UNICEF, SIO da wasu abokan hulɗa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending