News
Jami’an NAFDAC Sun Kama Magungunan Malaria Na Jabu Da Darajarsu Ta Kai Naira Biliyan 1.2
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta ce ta kama magungunan malaria na jabu da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2 a jihar Legas.
Daraktan Bincike da Aiwatarwa na hukumar, Martin Dotun, ya ce duk da ƙoƙarin da ake yi wajen yaƙi da magungunan bogi, wasu ƴan kasuwa marasa gaskiya na ci gaba da shigo da su cikin ƙasar. A cewarsa, an ɓoye magungunan cikin sassan motoci domin kauce wa jami’an tsaro.
Jihar Kano Za ta Kaddamar da Sabon Shirin Rigakafin Rubella: Hukumar PHC Ta Wayar da Kan Iyayen Yara
NAFDAC ta bayyana cewa jami’anta sun bi wata babbar mota daga hanyar Oshodi–Mile 2 har zuwa wani rumbun ajiya, inda aka gano katon 277 na magungunan da aka ɗora a matsayin kayan mota.
Hukumar ta ce wannan aiki na daga cikin jerin farmaki da ta gudanar a baya a kasuwannin Aba, Onitsha da Idumota, kuma za ta ci gaba da irin waɗannan matakai domin aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Daraktar Hukumar, Dr. Mojisola Adeyeye, na kare lafiyar ‘yan Najeriya daga haɗarin magungunan bogi.
Shugabar tawagar da ta jagoranci samamen, Florence Uba, ta ce an gudanar da aikin a ranar 29 ga Agusta 2025, inda aka gano cewa magungunan sun fito da lakabi daban-daban da za su iya ruɗar jama’a su saya a matsayin maganin malaria na gaskiya.
NAFDAC ta jaddada cewa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen kawar da wannan barazana daga Najeriya.
