News
An Cafke Wasu Mutane 6 Da Suka Tono Gawa A Kabari Tare Da Cire Sassan Jikinta Don Yin Asiri A Gombe
Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum shida bisa zargin tono gawar wani mutum a kabari tare da cire sassan jikinta domin yin asiri.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Kawuji Sarki, mai shekaru 39, ya amsa laifin.
Ranar Masu Fama da Cutar Laka: Gwamnatin Kano da Kungiyoyi Sun Jaddada Muhimmancin Tallafi
Ya bayyana cewa wani mutum mai suna Aliyu Chindo ne, ya ba su aikin cire idanun mamacin, tare da yi wa kowannensu alƙawarin Naira 500,000.
Sai dai ya ce bayan kai masa sassan jikin, Chindo ya gudu ba tare da ya biya su ba.
Nan take jami’an tsaro suka cafke su.
An gano cewa sun tono kabarin wani tsoho mai shekaru 85, Mallam Manu Wanzam, wanda aka binne a ranar 9 ga watan Satumba a maƙabartar Gadam Arewa da ke Ƙaramar Hukumar Kwami.
Kakakin NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya bayyana sunayen sauran da aka kama: Adamu Umar (22), Umar Jibrin Aboki (21), Abdullahi Umar Dauda (17), Muhammed Isa Chindo (28), da Manu Sale (23).
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da neman Aliyu Chindo da ya tsere.
Kwamandan hukumar a jihar, Jibrin Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “rashin imani,” tare da tabbatar da cewa za su gurfanar da waɗanda suka kama a kotu bayan kammala bincike.
