Connect with us

News

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar ’Yarta ’Yar Shekara 10 Kan Zargin Maita A Bauchi ‎

Published

on

images

Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau, Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda bayan da ta ƙona al’aurar ’yarta ’yar shekara 10, kan zargin maita.

Rahotanni sun nuna cewa matar ta dumama cokali a wuta, ta kuma umarci ’ya’yanta biyu su riƙe yarinyar kafin ta yi amfani da cokali wajen ƙone ta. Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama da matsalolin fitsari da bayan gida.

Advertisement

An Cafke Wasu Mutane 6 Da Suka Tono Gawa A Kabari Tare Da Cire Sassan Jikinta Don Yin Asiri A Gombe 

Maƙwabta ne suka kai ƙarar matar ga ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) domin kula da lafiyarta.

Kakakin rundunar ’yan sandan Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da kama matar da wasu, ciki har da wata mai maganin gargajiya, Fatima Abdullahi, wadda ta karɓi kuɗin matar sannan ta tabbatar mata cewa yarinyar mayya ce.

Advertisement

An bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar 11 ga Satumba, 2025. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci.

Rundunar ’yan sanda ta kuma gargadi iyaye da su daina kai ’ya’yansu wajen bokaye ko masu maganin gargajiya, tana mai jaddada cewa irin wannan dabi’a na iya haifar da ɓarna maimakon waraka.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending