Connect with us

News

‎Akwai Fargabar Sama Da Mutane 100 Sun Mutu Bayan Rugujewar Ramin hakar Zinare A Zamfara

Published

on

Akalla Mutane 33 Sun Mutu A Wani Wurin Hakar Ma’adanai A Birnin Tehran

Aƙalla mutane 100 ake fargabar sun mutu bayan rugujewar wani ramin hakar zinare a ƙaramar hukumar Maru, Jihar Zamfara, kamar yadda shaidu da mazauna yankin suka bayyana.

‎Rahotanni sun nuna cewa ramin dake wurin hakar ma’adinai na Kadauri ya ruguje ne da daddare a ranar Alhamis, a lokacin da daruruwan ma’aikata ke cikin ƙasa suna aiki.

Advertisement

Stallion Times Da NUJ Sun Horar Da ’Yan Jaridu Kan Yadda Za Su Yi Amfani Da Fasahar AI 

‎Wani mazaunin yankin, Sanusi Auwal, wanda ya shiga aikin ceto, ya ce an fitar da gawarwaki 13 daga cikin ramin, ciki har da na ɗan uwansa. “Fiye da mutane 100 ne suka kasance a cikin ramin lokacin da ya ruguje,” in ji shi.

‎Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara (ZSEMA), Ambasada Bala Ahmad, ya tabbatar da faruwar hatsarin a Gusau ranar Juma’a. Ya ce ramin ya rufeta  a  wasu ramin  hakar ma’adinai na gargajiya, amma bai bayar da ƙarin bayani ba.

Advertisement

‎Shugabannin al’umma sun ce daruruwan mutane sun makale a ramukan saboda ruwan sama mai yawa da aka samu a yankin kafin rugujewar. Ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ko suka makale ba tukuna.

‎Ana ci gaba da kai waɗanda suka samu raunuka zuwa Asibitin Maru domin samun kulawa, yayin da jami’an gwamnati da al’ummar yankin ke ci gaba da aikin ceto domin kubutar da waɗanda har yanzu ke makale.

Advertisement

 

 

Advertisement

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending