News
Yadda Fara Saukar Farashin Kayan Abinci Ya Tilasta Wa ’Yan Kasuwa Fito Da Kayayyaki Daga Rumbunan Su
A yayin da farashin kayan masarufi ya fara nuna alamun sauka a kasuwannin Najeriya, wasu ‘yan kasuwa sun fara fitar da kayayyakin da suka ajiye a rumbunansu da fatan kada su yi asarar riba.
Wani ɗan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa raguwar farashin kayan abinci, duk da cewa ba ta kai yadda ake fata ba, ta fara shafar kasuwanci sosai.
Akwai Fargabar Sama Da Mutane 100 Sun Mutu Bayan Rugujewar Ramin hakar Zinare A Zamfara
“Farashin kayayyakin masarufi na raguwa a ‘yan kwanakin nan. Ko da yake ba sauka sosai ake gani ba, amma dai sauka akwai. Wannan ce ta sa mu ’yan kasuwa ke fargabar ci gaba da ajiye kaya saboda tsoron kada mu yi asara,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Sabbin kaya kamar wake da sauran su sun fara zuwa kasuwa. Sannan ga farashi yana raguwa fiye da yadda aka saba gani a irin wannan lokaci a bara. Idan ba mu fito da kayanmu yanzu ba, ba mu siyar ba, ba mu san nan gaba farashin zai tsaya a ina ba.”
A cewarsa, wannan sauyi ya kawo sauƙi ga rayuwar jama’a, inda ya bayyana cewa:
“Al’umma suna jin daɗi saboda duk wanda ya zo kasuwa yanzu yana ganin sauƙi. Idan da mutum rabin kwano na shinkafa zai iya saya a da, yanzu zai iya sayen kwano ɗaya saboda raguwar farashin. Hakan shi ma yana ƙara mana riba.”
