Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Gudanar da Tsftar Muhalli da Wayar da Kan Jama’a kan Sauyin Yanayi

Published

on

IMG 20250927 WA0011

DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN

Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da zagayen tsftar muhalli da wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi a yau, Asabar 27 ga watan Satumba, karkashin jagorancin Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano. Wannan aikin na tsftar muhalli yana daga cikin shirye-shiryen da ake gudanarwa a karshen kowanne wata.

Advertisement

Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ya samu wakilcin Daraktan Tsare-Tsare da Kididdiga na Ma’aikatar, QS Shazali Garba Fagge, wajen kaddamar da aikin. A yayin da yake bayyana jin dadinsa, Shazali ya ce yana matukar farin ciki da yadda aikin ya gudana cikin tsari da doka, ba tare da wani anci mutunci ba.

Yadda Fara Saukar Farashin Kayan Abinci Ya Tilasta Wa ’Yan Kasuwa Fito Da Kayayyaki Daga Rumbunan Su

Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da lura da tsaftar muhalli a gidajensu da unguwanni, domin tabbatar da ingantacciyar lafiya da kuma kiyaye dokokin muhalli.

Advertisement

Daraktan Muhalli, yayin jawabi, ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin gwamnati da jama’a wajen tsaftace muhalli da rage illolin sauyin yanayi.

A wani bangare, Magistrate Auwal Yusuf, mai shari’a na kotun “Tafi da Gidan Ka”, ya yi kira ga jama’a musamman masu ababen hawa da su dinga bin ka’idojin zirga-zirga yayin da ake gudanar da tsftar muhalli, domin gujewa hatsari da rikice-rikice.

Advertisement

Wakiliyar mu, Safiya Muhammad Usman, ta ruwaito cewa kotun ta yankawa wasu daga cikin masu ababen hawa da aka kama yayin tsftar muhalli tarar Naira 260,000 sakamakon karya dokokin da suka yi. Wannan hukunci ya kasance a matsayin gargadi ga duk wanda zai kiyayewa tsaftar muhalli da dokokinta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending