Connect with us

News

‎A Kama Wani Uba Yana Yunƙurin Safarar ‘Yarsa Zuwa Ƙasar Waje

Published

on

Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama wani mahaifi yana yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi.

‎Mai magana da yawun hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Yan Bindiga Sun Sace Kansiloli Biyu Da Limami A Zamfara

‎Sanarwar ta ce mahaifin na daga cikin aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane waɗanda aka cafke a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

TRT ta ruwaito Adekoye na cewa an kuɓutar da mutum 24 a yayin aikin bisa jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello wanda aka gudanar bisa bayanan sirri da aka tattara.

‎Ya bayyana cewa a cikin waɗanda ake zargin akwai wani babban jami’in tsaro, wanda ke cikin masu safarar mutane a Kudu maso Yammacin Nijeriya.

‎Adekoye ya ce waɗanda aka kuɓutar ɗin yara ne da matasa waɗanda shekarunsu ke tsakanin shekara 15 zuwa 26 waɗanda aka ɗauko daga jihohin Kano da Katsina da Oyo da Ondo da kuma Ribas, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasashen Iraƙi da Sudan da Masar da Saudiyya da Bahrain da kuma Afghanistan.

Advertisement

‎Ɗaya daga cikinsu ta sha alwashin cewa sai ta tabbatar an gurfanar da mahafinta a gaban kotu kan yunƙarin safararta da ya yi zuwa iraƙi, in ji jami’in.

‎Ya ƙara da cewa, wata cikin waɗanda aka yi ƙoƙarin safarar ta ce mahafiyarta ce ta rinjaye ta ta yarda da cewa za ta tafi Turai domin yin aiki ta samu daloli.

‎Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bayyana damuwa game da ƙaruwar matsalar safarar mutane, musamman a lokacin da ake samun yawan ‘yan Nijeriya ke barin ƙasar.

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending