Connect with us

News

Ƙungiyar ASUU Ta Fara Haɗa Kan Mambobinta Domin Fara Yajin Aiki A Najeriya

Published

on

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta fara hada kan mambobinta dake jami’o’in kasar nan domin fara yajin aikin kasa baki daya.

Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan watsi da al’amuranta da gwamnatin tarayya ta yi duk da sanarwar da ta aika wa hukumomin da suka dace inda a ciki har da ministocin kwadago da ilimi.

Ƙungiyar SSANU Da NASU Za  Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, a wata wasika da aka fitar ranar 5 ga Oktoba, 2025, ya bayyan cewa babu wani ci gaba da aka samu na gwamnati ta biya bukatunta duk da cewa sun dade suna janyo sabani tsakanin gwamnati da kungiyar.

Idan ba a manta ba a kwanakin da suka gabata ASUU ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 14 don kammala yarjejeniyar da aka tsara tun watan Fabrairu, 2025 ko ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu idan ba a dauki mataki ba.

ASUU ta ce manufar yajin aikin ita ce tilasta gwamnati ta sanya hannu da aiwatar da sabuwar yarjejeniya, da kuma sake farfado da tsarin jami’o’in kasar domin gogayya da sauran kasashe.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending