News
Shugaba Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Waɗanda Aka Yi Wa Afuwar Shugaban Ƙasa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a cire sunan Maryam Sanda — wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekara ta 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello — daga cikin jerin waɗanda aka tanadi musu afuwar shugaban ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa Sanda na cikin jerin mutanen da ake tunanin za su samu rangwame, sai dai an soke sunanta bayan umarnin shugaban ƙasa da ya haramta bayar da afuwa ga waɗanda aka tabbatar da laifuka masu tsanani.
DSS Sun Cafke Wani Matashi Bisa Yin Kira Ga Sojoji Da Suyi Juyin Mulki A Shafin X
A cewar sabon umarnin, duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, safarar mutane, zamba, da kuma mallaka ko safarar makamai ba bisa ka’ida ba, ba za su sake cin gajiyar afuwar shugaban ƙasa ba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
