News
Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Martani Kan Rahoton Da Ya Zargi Jihar Da Tauye ’Yancin ’Yan Jarida
Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da Cibiyar Wole Soyinka ta wallafa, wanda ya zargi jihar da kasancewa cikin jihohin da ke keta ’yancin faɗar albarkacin baki na ’yan jarida a Najeriya.
A cewar gwamnatin, rahoton ba shi da tushe, hujja ko madogara, illa kawai ƙoƙarin ɓata sunan gwamnati da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke jagoranta.
Shugaba Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Waɗanda Aka Yi Wa Afuwar Shugaban Ƙasa
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Wayya, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Kano.
“Gwamnatin Kano tana mutunta ’yancin faɗin albarkacin baki bisa doka da tsarin mulki. Muna maraba da suka idan an gina ta bisa gaskiya da hujja, amma ba za mu lamunci ƙarya don ɓata suna ba,” in ji Wayya.
Rahoton Cibiyar Wole Soyinka mai taken “Shrinking Freedoms: 2024 Journalism and Civic Space Status Report” ya sanya Kano cikin jihohi uku da ake zargin suna tauye ’yancin ’yan jarida — tare da Lagos da Abuja.
Sai dai Wayya ya ce rahoton “ba shi da wata hujja ta sahihanci,” yana mai cewa cibiyar “ba ta da wakilai a Kano ko wasu jihohi da ke tattara sahihan bayanai.”
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin Gwamna Yusuf ta dage wajen kare kafafen yada labarai da tabbatar da dimokuraɗiyya, ta hanyar buɗe hanyoyin sadarwa da haɗin kai da ƙungiyoyin farar hula.
Ya kuma tunatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na daga cikin shugabannin da suka fi samun yabo daga ƙungiyoyi da kafafen yada labarai a Najeriya, ciki har da Jaridar Leadership, wacce ta bashi lambar yabo ta “Gwamna Mafi Himma Wajen Inganta Ilimi”, da kuma “African Governor of the Year for Good Governance” daga African Leadership Magazine.
“A shekarar 2024, lokacin zanga-zangar adawa da rashin kyakkyawan shugabanci a Najeriya, Gwamna Yusuf shi ne kadai a ƙasar da ya karɓi masu zanga-zanga da kyakkyawar niyya,” in ji Wayya.
Kwamishinan ya ce gwamnati za ta ci gaba da gudanar da al’amuranta cikin gaskiya da buɗaɗɗen tsarin da ke mutunta aikin jarida da ra’ayoyin jama’a.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
