News
Uwa Da ’Yarta Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Borno
Habiba Abubakar mai shekaru 35 da ’yarta Adama mai shekaru 9 sun rasa rayukansu bayan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Karamar Hukumar Hawul da ke Jihar Borno.
Mai magana da yawun Rundunar ’San Sanda ta jihar, Nahum Daso, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 1:15 na rana, yayin da suke komawa gida daga gona.
Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Martani Kan Rahoton Da Ya Zargi Jihar Da Tauye ’Yancin ’Yan Jarida
Ya ce, “Sun fito daga gona ne kuma suna ƙoƙarin ketare wani kogi da ke kusa da kauyen Ghung. Amma saboda ƙarfi da saurin ruwan, jirgin ruwan nasu ya kife a wani wuri mai zurfi na kogin.”
A cewarsa, jami’an ’yan sanda tare da masu aikin ceto a yankin daga bisani sun gano gawarwakin su daga cikin kogin.
“Ba a ga wata alama ta tashin hankali a jikin gawarwakin ba. An ɗauki hotuna don adana bayanai kafin a kai su Asibitin Garkida da ke Karamar Hukumar Gumbi a Jihar Adamawa, domin shi ne asibitin da ya fi kusa da su,” in ji Daso.
An mika gawarwakin ga iyalansu don yin jana’izar su bisa tsarin Musulunci.
“A halin yanzu, Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan jihar da ke Maiduguri ya fara bincike kan lamarin,” in ji Daso.
Aminiya ta ruwaito cewa a watan Satumba an gano gawar wani yaro mai sayar da kaya, wanda ake kyautata zaton ya kai shekaru 12, daga cikin kogin Gamboru da ke unguwar Customs a birnin Maiduguri, babban birnin jihar
A ’yan watannin nan dai ana samun yawan nitsewar jiragen ruwa musamman a yankin Arewa maso Gabas na ƙasar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
