Connect with us

News

Dakarun Sojin Ruwan Ghana Sun Kama ‘Yan Nijeriya 10 Da Suka Ɓuya A Jirgin Ruwa

Published

on

d31a9a41247b6b18a5588fe2d9db1ba06137ab16bb6613a05c87fe75a3075308
Spread the love

Rundunar sojin ruwan Ghana ta kama ‘yan Nijeriya da suka yi yunƙurin balaguro a ɓoye a cikin wani jirgin ruwa mai ɗauke da tutar ƙasar Panama, MV Grand Venus, a tashar jiragen ruwa ta Tema.

Wata sanarwa daga rundunar sojin Ghana (GAF) ta ce an yi kamen ne ranar Jumma’a 31 ga watan Oktoban shekarar 2025, bayan an samu kiran neman ɗauki daga jirgin.

Jami’an Tsaro Sun Kama Mutum Da Wayoyi 17 Na Sata A Wurin Sauya Shekar Gwamnan Bayelsa

Bincike ya nuna cewa mutanen sun shiga jirgin ruwan ne a asirce a lokacin da ya tsaya a tashar jiragen ruwa ta Nijeriya da ke Legas.

“Rundunar sojin ruwan Ghana a ranar Jumma’a , 31 ga watan Oktoban shekarar 2025, ta kama mutum 10 masu tafiya a ɓoye cikin wani jirgin ruwa mai ɗauke da tutar Panama Grand Venus a bayan an samu kiran neman ɗauki,” in ji sanarwar.

Advertisement

Bayan kamen, rundunar sojin ruwan Ghana ta raka jirgin ruwan zuwa tashar jiragen ruwan inda ta miƙa waɗanda ake zargin ga hukumomin da lamarin ya shafa ciki har da masu kula da tashar jiragen ruwa da hukumar shige da ficen Ghana da kuma ‘yan sandan ruwa domin ƙarin bincike.

Rundunar sojin ta tabbatar wa jama’ar ƙasar cewa za ta yi ƙarin bayani yayin da ake ci gaba bincike.

“Rundunar sojin ruwan Ghana tana so ta tabbatar wa mutane cewa za ta yi ƙarin haske yayin da bincike ke ci gaba,” in ji sanarwar.

 

Advertisement

TRT GLOBAL

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *