Connect with us

News

Yerima Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Kwanaki Bayan Cacar Baka Da Wike

Published

on

imyerimaages 1
Spread the love

Wasu rahotanni daga Najeriya sun ce sojan da ya yi cacar baka da ministan Abuja, Laftanar Ahmed Yerima ya tsallake rijiya da baya yammacin yau, lokacin da wasu mutanen da ake zargin mahara ne suka yi ƙoƙarin kai masa hari

Jaridar Vanguard da ake wallafawa a ƙasar, ta ce majiyar soji sun tabbatar mata cewar wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya a cikin wasu motoci ƙirar Hilux guda biyu da basu da lamba sun yi ta bibiyar Yarima daga gidan man NIPCO a kan hanyar Gado Nasco.

Civil Society Groups Celebrate Dr. Sami Charles’ Birthday, Urge Him to Return to Nigeria to Support National Development

Majiyar ta ce sojan ya fahimci cewar ana bin sa, sai ya yi dabarun su na soji domin kauce musu da misalim karfe 6.30 na yammacin yau, abinda ya kai ga shaidawa hukumomin su na soji.

Majiyar ta bayyana cewar, hukumar soji na ɗaukar lamarin da girma, kuma ta na gudanar da bincike a kai, ba tare da gabatar da cikakkun bayanai ba, domn kaucewa gabatar da bayanan asiri.

Advertisement

Wannan lamari na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan cacar bakan da sojan ya yi da ministan Abuja Nyesom Wike a kan wani fili da tsohon babban hafsan sojin ruwa na ƙasa ya mallaka a ƴankin Gaduwa.

Tuni bidiyon cacar bakan ya karaɗe duniya, inda mutane da dama ke ci gaba da bayyana ra’ayoyin su, yayin da fadar shugaban ƙasa ta shiga cikin lamarin.

Daga cikin manyan hafsoshin sojin da suka bayyana goyan bayan su ga Yarima harda shugaban sojin ƙasa, Janar Yusuf Tukur Buratai da Janar Lucky Irabor.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *