Connect with us

News

Gobara Ta Yi Ajalin Yara Biyu ’Yan Gida Ɗaya

Published

on

Wata gobara da ta tashi a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas ta yi ajalin yara biyu ’yan gida ɗaya, a wajen da daruruwan mutane suka rasa matsugunninsu.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da mahaifiyar yaran ta fita sayen kayan girki, ta bar ’ya’yanta huɗu a ɗaki da ta rufe Kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito

Advertisement

Jami’an ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyu da suke barci ba su samu damar tserewa ba, inda gobarar ta kone su kurmus. Sauran biyun da suke farke sun tsere kafin wutar ta yi muni.

Shaidu sun ce sun hango hayaƙi yana tashi ne suka hanzarta kiran ma’aikatar kashe gobara, domin dakile wutar kada ta bazu zuwa sauran gidaje.

Advertisement

Wani mazaunin yankin ya ce ba gaskiya ba ne zancen da ya yadu a kafafen sada zumunta cewa gobarar ta tashi ne a harabar Kwalejin Captain Elechi Amadi. Ya bayyana cewa wutar ta tashi ne a bayan makarantar, a wani yanki da ke cike da dogayen gidaje da iyalai sama da 27 ke zaune.

Ya ce gobarar ta ƙone dukiyoyi masu daraja, abin da ya jefa mutane da dama cikin halin rashin matsugunni.

Advertisement

Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce yaran biyu da suka mutu shekarunsu na tsakanin biyar zuwa tara.

Ta ce an fara bincike don gano musabbabin gobarar, kuma an gayyaci mahaifiyar yaran domin amsa tambayoyi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending